
Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN ta goyi bayan kasar Amurka da ta ce ana kashe kiristoci a Najeriya da yawa.
Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh ne ya bayyana hakan ranar Laraba.
Yace kin fadawa kai gaskiya da zargi ba zai kawo karshen matsalar ba
Yace karfin hali da fuskantar matsalar tare ne zai kawo yadda da juna a tsakani.
Yace tabbas Kiristoci a sassa daban-daban na Najeriya musamman yankunan Arewa na fuskantar Kisa da asarar Dukiyoyi da sauransu.
Sanatan kasar Amurka, Ted Cruz ne ya bayyana hakan inda yayi zargin cewa an kashe Kiristoci 52,000 da kona coci-coci 20,000 a Najeriya.
Gwamnatin Tarayya dai Tuni ta karyata wannan ikirarin na satan kasar Amurkar.