
Jirgin saman da ‘yan kwallon Najeriya, Super Eagles ke ciki yayi saukar gaggawa bayan da gilashin gaba na jirgin ya tsage.
Jirgin ya saukane a kasar Angola.
‘Yan wasan na dawowa ne daga wasan da suka buga da Lesotho wanda suka yi nasara 2-1.
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, (NFF) ta tabbatar da hakan inda tace direban jirgin yayi kokari sosai wajan saukar da jirgin bayan faruwar lamarin.