Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa, dan an zageshi baya fitowa ya kare kanshi.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya wallafa inda yace shi sai idan an taba addini ne yake fitowa yayi martani.
Malam Daurawa yace tarbiyyar da malaminsu ya koyar dasu kenan inda yace su baiwa addini Kariya su kuma Allah zai basu kariya.