
Matashi me amfani da sunan Sarki a X ya bayyana cewa, a shirye yake ya auri Maryam Sanda a matsayin mace ta biyu.
Ya bayyana hakane bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mata afuwa.
Maryam Sanda dai ta kashe mijinta ne wanda dalilin haka kotu ta yanke mata hukuncin kisa.
Saidai a cikin jerin wadanda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya wa Afuwa an ga sunan Maryam Sanda.
Wasu dai sun alakanta wannan afuwa da cewa kudi ne suka sa aka mata inda wasu ke cewa, Hanya ce.