
Rahotanni sun ce tuni shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara neman wanda zai maye ministan Kudi, Wale Edun dashi.
Ministan Kudi, Wale Edun ya kwanta rashin lafiya bagtatan inda rahotanni suka ce shanyewar rabin jiki ce ta kamashi.
Rahotannin sun ce an garzaya dashi zuwa kasar waje.
Hakanan rahotannin sun ce ko da ya warke da wuya ya iya komawa bakin aikinsa.
Wannan ne yasa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara meman wanda zai maye gurbinsa dashi.
Rahotanni sun ce Shugaba Tinubu ya baiwa Gwamnan Babban bankin Najeriya, CBN umarnin maye gurbin Ministan kudin a wai taro da za’a yi a kasashen waje.