
‘Yar Najeriya, Tsohuwar Tauraruwar BBNAIJA, Natacha Akide wadda aka fi sani da Tacha ta yiwa mutane 145 kwalliya a cikin awanni 24 dan ta shiga kundin tarihin Duniya.
Ta aikata hakanne a Legas inda aka dauke ta Bidiyon yayin da take aikata hakan.
Duk da cewa an samu matsalar daukewar wuta amma tasha ta kammala wannan abu nata Lafiya.