
Mahaifin mijin Maryam Sanda, Alhaji Ahmed Bello Isa ya bayyana cewa, shine ya roki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yafewa matar dansa duk da itace ta kashe dan nasa.
Alhaji Ahmed Bello Isa yace aiwatarwa da Maryam Sanda hukuncin kisa ba zai dawo da dansa,Bilyaminu Bello ba.
Yace maimakon haka ya zabi yafe mata dan a saketa ta kula da ‘ya’yanta kanana.
Ya bayyana hakane yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Talata wadda suka gudanar shi da mahaifin Maryam Sanda, Alhaji Garba Sanda