
Rahotanni daga jihar Katsina sun bayyana cewa, wani jami’in Kwastam me suna Lawal Tukur me mukamin Assistant Superintendent of Customs (ASC) ya rigamu gidan gaskiya a wani dakin Otal.
Kafar Zagazola makamace ta wallafa labarin inda tace jami’in Kwastam din ya rasu ne a dakin Otal din Murjani Hotel ranar 15 ga watan October.
Zagazola makama sun ce Ma’aikatan otal din sun tarar da gawar jami’in kwance a dakin da ya kama da misalin karfe 8:30 a.m.
Zagazola makama sunce kamin rasuwarsa wasu mata 3 sun ziyarceshi a dakin, matan sune kamar haka, Khadija Ali me shekaru 34, wadda ta fito daga Dutsen Amare Quarters dake jihar ta Katsina, sai A’isha Lawal me shekaru 30 wadda ta fito daga karamar hukumar Ingawa, Sai Hafsat Yusuf me shekaru 22 wadda ta fìto daga Brigade Quarters jihar Kano.
Rahotannin sunce Khadija da Aisha sun kwana tare da marigayin a dakin Otal din inda daga baya Hafsat itama ta shiga dakin.
An garzaya da gawar mamacin zuwa Federal Medical Centre (FMC) dake Katsina inda likitoci suka tabbatar da ya mutu sannan an kai gawar zuwa Mutuware dan gudanar da bincike.
Hukumar Kwastam din ta tabbatar da lamarin.