
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Lura da irin Arzikin ma’adanan karkashin kasa da Allah yawa kasarnan, bai kamata ace akwai talaka a kasarba
Shugabab ya bayyana hakane a wajan taro kan Arzikin ma’danan karkashin kasa da Allah yawa Najeriya da ya gudana a Abuja.
Sakataren Gwamnatin tarayya, George Akume ne ya wakilci shugaban kasar a wajan taron.
Ya bayyana cewa, Gwamnatin tarayya zata yi dukkan mai yiyuwa wajan samar da yanayi me kyau na zuba hannun jari a kasarnan ta bangaren ma’adanan karkashin kasa.
Sannan ya yi kira ga kasashen Afrika dasu yi amfani da ma’adannan karkashin kasar da Allah ya hore musu dan karfafa tattalin arzikin su.