
Matashi Abubakar dan jihar Borno wanda yayi ridda ya koma Kirista ya bayyana cewa, ba gaskiya bane labarin da ake yadawa cewa kudi aka bashi ya koma kirista.
Yace bincikene yayi ya gano gaskiya.
Yace yanzu abinda yake so shine a samu malamai su nuna masa inda aka cewa, Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi sallah sau biyar a Qur’ani.
Yace idan aka nuna masa zai sake komawa Musulunci.