
Kungiyar Kwadago ta kasa, NLC ta gargadi Gwamnatin tarayya da cewa, ta basu sati 4 su daidaita da kungiyar malaman jami’a ta ASUU.
Kungiyar tace idan kuwa ba’a samu daidaiton ba to suma zasu tsunduma yajin aiki su taya kungiyar ASUU din.
Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja inda yace kuma suna Allah wadai da kin biyan ma’aikatan ASUU din albashi saboda su shiga yajin aiki.
Yace ba zasu kara bari a wulakanta wata kungiyar Kwadago ba suna gani.