
Tauraron me wakokin batsa da ‘yan mata tsirara-tsirara, Soja Boy ya bayyana cewa duk da zagin da ake masa kan wakokinsa, da zai fito yace zai yi aure mata sai ya ture.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi ta kai tsaye a Tiktok inda aka tambayeshi ko ya zai so matar da zai aura ta amince ya ci gaba da abinda yake yi?
Yace ko da bai samu matar aure ba anan Najeriya, zai iya zuwa kasashen Turawa ya yi aure.
Amma yace anan ma duk da zagin da ake masa idan ya fito neman aure yasan mata sai ya ture.