
Rahotanni daga jihar Naija na cewa, an kama wani dalibin jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida University saboda zargin ya soki gwamnan jihar, Mohammed Umar Bago.
Sunan dalibin da aka kama Abubakar Isah Mokwa kuma an kamashine ranar Alhamis a dakinsa dake garin Lapai.
An kamashine bayan da yayi rubutu yana sukar Gwamnan Gwamnan a shafinsa na Facebook.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da kamen inda yace suna kan binciken wanda akw zargin.