
Rahotanni sun ce jami’an soji sun kai samame gidan tsohon Ministan man fetur a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari watau Timipre Sylva dake Abuja.
Rahoton na Sahara reporters yace jami’an tsaron sun yiwa gidan kacha-kacha inda suka kuma tafi da wani dan uwan tsohon Ministan.
Rahoton yace Ministan tuni ya bar Najeriya tunda aka fara mai wadannan zarge-zargen.
Hakanan Rahoton yace an kuma kaiwa gidansa na Bayelsa samame.
A baya dai an bayyana cewa akwai wani tsohon gwamnan Najeriya wanda shine ake zargin ya dauki nauyin yiwa shugaba Tinubu juyin mulki.