
Mutane 2 ne suka rasu wasu da dama suka samu raunuka sanadiyyar fadan da ya barke tsakanin musulmai a saboda tababar wanene zai yi limancin masallacin Juma’a na garin Donga dake jihar Taraba.
Daily Trust ta ruwaito cewa bayan asarar rayuka da jikkata wasu an kuma tafka asarar dukiya
Saidai Tuni an kai jami’an tsaro garin kamar yanda rahoton ya nunar.
An yi kokarin jin ta bakin kakakin ‘yansandan jihar, ASP Leshen James amma abu yaci tura.