
Duka ‘yan majalisar wakilai da suka fito daga jihar Enugu sun bar jam’iyyar PDP zuwa APC.
Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas ne ya sanar da haka a zaman majalisar na ranar Alhamis.
Gwamnan jihar Enugu, Peter Mba ya shaida wannan lamari a majalisar.
‘Yan majalisar sun ce sun koma APC ne saboda jam’iyyar su ta PDP rikicin cikin gida na neman gamawa da jam’iyyar.