
Rahotanni sun ce a cikin sojojin da aka kama da zargin yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki, SB Adamu ne aka baiwa aikin Shekye babban me baiwa shugaban kasa, shawara kan tsaro, watau Malam Nuhu Ribadu.
Shi dai SB Adamu an kaishi aiki ofishin Malam Nuhu Ribadu wanda kuma aka bashi aikin ya kula dashi ya shekye.
Kafar Thecable ce ta ruwaito labarin inda tace wata majiyar gidan soji ce ta sanar da ita hakan.
Tace ba kamar yanda ake yadawa cewa sauran sojojin da suka shirya juyin mulkin a ofishin me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro suke ba, tace SB Adamu ne kadai a ofishin.
Majiyar sojin tace wannan alamace dake nuna cewa masu juyin mulkin sun kama manyan sojoji sosai a gidan sojan.