
A kwanakin da suka gabata ne Ministan Kudi, Wale Edun ya kwanta rashin lafiya inda har ta kai ga an kaishi kasar Ingila dan ya ga Likitocin sa.
Sahara reporters sun ce yanke jiki yayi ya fadi saidai gwamnati ta musanta hakan amma daga baya Gwamnatin ta tabbatar da rashin lafiyar ministan.
A yanzu sabon Labari da Sahara reporters din suka samu shine cewa, Ministan Kudin, ya ga sunanshi a cikin jerin sunayen wadanda sojojin da suka shirya juyin mulki zasu kashene, abinda ya firgitashi kenan ya yanke jiki ya fadi sumamme.
Rahotan yace Wale Edun shine Mutum na 4 a cikin jerin wadanda Sojojin da suka shirya Jhuyin mulkin suka so shekyewa.