Tuesday, November 11
Shadow

Da Duminsa:Kotu ta kwace kujerar dan majalisar wakilai daga jihar Zamfara bayan da ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta kwace kujerar dan majalisar wakilai, Abubakar Gummi bayan da ya bar jam’iyyar PDP zuwa APC

Abubakar Gummina wakiltar mazabun Gummi/Bukkuyum ne a majalisar wakilai ta tarayya.

Mai shari’a, Obiora Egwuatu ne ya yanke wannan hukunci inda yace kada kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya sake kallon Abubakar Gummi a matsayin dan majalisar.

Hakanan alkalin ya kuma baiwa hukumar zabe me zaman kanta INEC umarnin sake shirya wani zabe dan cike gurbin dan majalisar nan da kwanaki 30.

Karanta Wannan  Bello El-Rufai da Sadiq Zololo sun sayi Kungiyar kwallon kafa ta Ranchers Bees

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *