
Rahotanni sun ce an gano Naira Biliyan 11 a asusun daya daga cikin sojojin da ake zargi da yunkurin yiwa shugaba Tinubu Juyin mulki.
Rahotan yace sojan me mukamin Colonel ne kuma yana aiki ne a karkashin wani soja me mukamin Brigadier General.
Dda aka tambayeshi, yace kudin na wani tsohon Gwamna ne kuma kasuwanci suke shi da gwamnan.
Rahoton ya kara da cewa a baya an taba kai sojan aiki a yankin Naija Delta.