
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa nan gaba kadan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai gana da shugaban kasar Amurka, Donald Trump.
Me baiwa shugaban kasar shawara kan harkar sadarwa, Daniel Bwala ne ya bayyana hakan.
Yace a kwai kyakkyawar alaka tsakanin Najeriya da Amurka inda yace a baya Amurkar ta sayarwa Najeriya da makamai Wanda ta yi amfani dasu wajan yakar matsalar tsaro.
Hakan na zuwane kwana daya bayan da shugaban Amurkar, Donald Trump yayi barzanar kawo hari Najeriya idan gwamnati bata dauki mataki kan harkar tsaro ba.