
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta musanta Rahoton dake cewa shugaban kasar zai gana da shugaban kasar Amurka, Donald Trump.
Wani Rahoto da Sahara Reporters suka ruwaito sun ce sun samu daga fadar shugaban kasa cewa shugaba Tinubu zai gana da mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance a ziyarar da zai kai kasar.
Saidai fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu tace ba gaskiya bane, kuma idan ma shugaba Tinubu zai je kasar Amurka, da shugaban kasar, Donald Trump zai gana ba da mataimakinsa ba.