
Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN ta bayyana cewa, da yawa basu fahimci kalaman Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ba.
Kungiyar reshen jihohin Arewa 19 da Abuja ta bakin shugabanta, Rev. John Joseph Hayab ne ta bayyana hakan.
Yace Ba ‘yan Najeriya Trump yace zai kawowa hari ba, cewa yayi zai kawowa ‘yan ta’adda harine, yace to menene na tayar da hankali inda ba mutum yasa yana da alaka da ‘yan ta’addan ba?
Yace wannan lamari kamata yayi ya zama hanyar da zata sa mu gyara matsalar tsaron mu ba wai ta zama hanyar cece-kuce akan addini ba.