
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC na neman tsohon karamin Ministan man fetur kuma tsohon Gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva ruwa a jallo.
EFCC a wata sanarwa data fitar tace tana neman Sylva ne bayan umarnin wata kotu a Legas ranar 6 ga watan Nuwamba inda ake zarginshi da yin canjin Dala $14,859,257 ba bisa ka’idaba.
EFCC tace duk wanda ya ganshi ya gaggauta sanar da ofishinta mafi kusa ko kuma ofishin ‘yansanda.
Timipre dai ne ake zargin ya dauki nauyin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Jhuyin mulki wanda aka dake a kwanannan.