
Hankula sun tashi akaita musayar yawu bayan da sojoji suka hana Ministan Abuja, Nyesom Wike shiga wani fili da ake rikici akansa.
Sojojin sunce shugabansu, Shugaban Sojojin Ruwa watau Vice Admiral Zubairu Gambo ne ya basu umarni.
Saidai Shugaban tsaro na kasa ya shiga lamarin aka sasanta kamin abun ya kazance.