Friday, December 5
Shadow

Akwai Hanyoyin Shigowa Najeriya guda 1,978 amma guda 84 ne kawai jami’an tsaro ke gadi>>Majalisar Tarayya ta koka

Dan majalisar wakilai Hon. Isa Mohammed Anka wanda shine shugaban Kwamitin majalisar wakilai dake kula da iyakokin Najeriya ya koka da cewa akwai hanyoyin Shigowa Najeriya daga kasashen waje guda 1,978 amma guda 84 ne kadai jami’an tsaro ke kula dasu.

Ya bayyana hakane ranar Talata a Abuja wajan kaddamar da kwamitin na wucin gadi.

Ya kara da cewa, wannan matsalar itace tasa ake samun yawan safarar mutane da miyagun kwayoyi da makamai da sauran abubuwan laifi.

Yace abinda yasa Gwamnati bata iya samar da tsaro sosai a wadannan hanyoyin shigowa Najeriya sun hada da karancin kudi, da sarkakkiyar hanyoyin da karancin ma’aikata.

Karanta Wannan  An Nad'a Matashi Dan Shekara 25 Sarki A Jihar Jigawa

Ya jinjinawa jami’an Kwastam, dana Immigration wajan kokarin da suke na kare Najeriya akan iyakoki inda yace akwai bukatar hadin kan sauran jami’an tsaron Najeriya dan samar da tsaro akan iyakokin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *