Wednesday, September 2
Shadow

Zhagin da Wike yawa matashin soja cin fuska ne ga Sojan, dama shugaba Tinubu>>Inji Buratai

Tsohon Shugaban sojojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa, zagin da Ministan Abuja, Nyesom Wike yawa matashin soja da ya hanashi shiga wani Fili dan ya rusashi cin fuskane.

Buratai yace dolene a rika girmamawa da kuma sanya jami’an soji a gaba a kasarnan.

Yace tsaro shine ke zuwa farko kuma zagin da Wike yawa matashin sojan cin fuskane da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Sojan da hukumar sojojin Najeriya.

Buratai yace dolene Wike ya fito ya baiwa matashin sojan hakuri, da shugaba Tinubu, dama Hukumar soji.

Yayi kira ga shugaba Tinubu da ya dauki matakin da ya dace akan lamarin.

Karanta Wannan  'Yan darika Taron Yuyu ne, Duk Kano, babu Majalisin da ya kai na Gadon kaya cika, Dan haka Me Girma Gwamnan Kano kada ka yadda su ce maka bamu da yawa>>Inji Malam Kan neman da ake Gwamnatin Kano ta dauki mataki kan Malam Lawal Triumph

Wike dai ya zagi wani matashin soja ne da ya hanashi shiga wani fili wanda na sojoji ne dan hana ci gaba da gini a filin, sojan yace an bashi umarnine.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *