
Rasuwar malamin Addinin Islama, Dan Dariqa, Abulfatahi Sani Tijjani ta zo da cece-kuce.
Mahaifiyar tasa ta rasu kuma an yi jana’izar ta kamar yanda addinin Addinin Musulunci ya tanada.
Saidai wasu matasan ‘yan Izala sun rika murna da rayuwarta inda wasu ke fadin cewa Tana Whuta.
Hakan yasa wasu malaman Izalan suka fito dan jan Hankali da fadar cewa matasan Izalan su daina irin wannan abu ba koyarwar sunnah ce ba.
Matasan na Izala dai na mayar da martanine kan irin abinda Abulfatahi yayi bayan rasuwar Marigayi Sheikh Abdulaziz Dutsen Tanshi.