
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa Sojan Ruwa da ya hanashi shiga wani Fili Jiya bashi da da’a sannan yana da girman kai.
Ministan ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunsa, Lere Olayinka a yayin da ake hira dashi a gidan talabijin na Channels TV.
Yace abin mamaki shine yanda ko da aka kira shugaban sojoji CDS aka baiwa sojan bai wani nuna kaduwa ba.
Lamarin rikicin Wike da Sojan ne babban labarin da ake ta tattaunawa akansa a fadin Najeriya.