
Rahotanni sun ce wani barawo ya lababa cikin gidan Gwamnatin Kano ya sace daya daga cikin motocin dake bin ayarin tawagar Gwamnan, Kano Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida.
Hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, watau Bashir Ahmad ne ya wallafa hakan a shafinsa na X inda ya kara da cewa wannan abin mamaki ne.