
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana cewa, sai da suka gargadi Wike kada ya je ya fuskanci sojan ruwa, A. Yerima ya bari sojoji su kammala bincikensu akan filin amma yaki ya.
Yace abinda sojan yayi ya aikata daidai bai aikata laifi ba domin yana bin umarnin na sama dashi ne.
Yace kuma jami’an gwamnati su guji wulakanta sojoji dan yin hakan kamar wulakanta shugaban kasa ne.
Yace Wike bai kamata ace yayi ja in ja da matashin sojan ba, kamata yayi ace ya nemi manyan sojan yayi magana dasu.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a DCL Hausa.