Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Mutum daya ya rigamu gidan gaskiya, wasu suka jikkata a Turmutsitsun daya faru a gidan karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle dake jihar Zamfara

Turmutsutsu a gidan karamin ministan tsaro dake Gusau jihar Zamfara, Bello Matawalle yayi sanadiyyar rasa rai daya wasu mutane 6 suka jikkata da yammacin ranar Alhamis.

Rahotanni sun ce lamarin ya farune da misalin karfe 7:30 na ranar Alhamis yayin da mutane suka taru a gidan nasa dan tarbarshi.

Zagazola Makama yace wanda ya rasun sunansa, Khalifa Uzairu kuma dan kimanin shekaru 23 ne.

Sannan akwai mutane 6 Ayuba Sani, Muhammadu Adams, Aliyu Aminu, Shaaban Hamisu, da Inusa Musa Shehu da su kuma suka jikkata suna karbar magani.

An kai jami’an tsaro wajan sannan an fara binciken yanda lamarin ya faru.

Karanta Wannan  Matatar Ɗangote ta sake rage farashin man fetur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *