Man Kanunfari an dade ana amfani dashi wajan magance matsalar rashin kuzarin namiji wajan jima’i.
Yana kara karfin Azzakari kuma yana karawa namiji kuzari wajan gamsar da mace a gado.
Idan mutum na fama da matsalar kawowa da wuri yayin saduwa da iyali, ana amfani da Kanumfari wajan magance wannan matsala.
Hakanan idan mazakutar mutum bata mikewa, shima Kanunfari yana taimakawa sosai wajan magance wannan matsala.
Idan mutum yana son karfin sha’awarsa ta karu, to yana iya amfani da Kanunfari wajan karawa kansa karfin sha’awa.
Yawanci amfanin Kanunfari yana bangaren kara karfin Azzakarine da kuma karawa namiji kokari sosai wajan gamsar da iyalinsa.
Hanyoyin da ake amfani da Kanunfani sune:
Ana iya mayar dashi gari, kamar na yaji ko a hadashi da yaji a rika barbasawa a abinci.
Ana kuma iya yin shayinsa, watau a rika tafasashi ana tsiyaye ruwan a kofi ana sha.
Ana hada ruwan shayin Kanunfari da zuma a sha, shima yana taimakawa namiji sosai wajan kara karfin Azzakari.
Saidai kamar yanda aka sani, duk wani abu dake da amfani yana kuma da rashin amfani, kada a rika shan Kanunfari da yawa ko kuma a rika shafa mansa da yawa, a rika yi a hankali.