Friday, December 5
Shadow

Jam’iyyar PDP ta kori Nyesom Wike

Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta sanar da korar ministan Abuja, Nyesom Wike, da wasu jiga-jiga daga cikinta, saboda abin da ta kira yi wa jam’iyya zagon-ƙasa.

Cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce ta ɗauki matakin ne domin kawo haɗin kai da ladabtarwa a jam’iyyar da kuma mayar da hankali ga zaɓukan 2027 masu zuwa.

Sauran mutanen da jam’iyyar ta kora sun haɗar da Samuel Anyanwu da Kamaldeen Ajibade da Ayo Fayose da Austin Nwachukwu da kuma wasu.

Sanarwar ta ce matakin ya samu amincewar mafiya rinjayen wakilan jam’iyyar da ke halartar babban taronta na ƙasa da ke gudana a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Karanta Wannan  Ina daf da ficewa daga PDP - Gwamnan Akwa Ibom

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *