
Babban lauya, Femi Falana(SAN) ya baiwa ‘yan Najeriya shawarar cewa, kar su sake yadda daga yanzu duk wanda aka sake yin Garkuwa dashi ya biya kudin fansa, ya kai Gwamnati kara ta mayar masa da kudinsa.
Yace dalili kuwa shine, Gwamnatin ta kasa bisa hakkin dake kanta na samar da tsaro ga ‘yan kasa dan haka ya kamata a kalubalanceta.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro da ya gudana a jami’ar Yakubu Gowon University dake Abuja.