
Tauraron fina-finan Hausa, Adam a Zango yayi godiya bayan da aka masa nasihar ya daina rawa da waka da film ya canja sana’a.
Daya daga cikin masu nasiha a Tiktok ne ya jawo hankalin Adam A. Zango da cewa, Allah yana sonsa musamman ma yanda yafi jarabarsa fiye da sauran taurarin masana’antar Kannywood.
Ya baiwa Adam A. Zango shawarar ya bude shago ya fara kasuwanci wanda yace idan ya saka Allah a gaba, zai ga nasara.
Adam A. Zango ya bayyanawa matashin cewa ya gode da Nasiha.