
Rahotanni na fitowa cewa hukumar ‘yansandan Farin kaya ta DSS yi gargadin cewa ana shirin kai wa makarantar ‘yan mata ta MAGA dake jihar Kebbi hari.
Gwamman jihar Kebbi, Mohammed Nasir Idris ya tabbatar da cewa DSS sun sanar dasu game da gargadin kuma suka bayar da shawarar a gudanar da taron tsaro kan lamarin.
Gwamnan yace sun gudanar da taro akan tsaro aka kai jami’an tsaro makarantar dan su tsare daliban amma sai suka buge da daukar hotuna da dalibai ‘yan mata ‘yan makarantar.
Gwamnan yace mintuna 30 kamin a kai harin, jami’an tsaron dake baiwa makarantar kariya sun janye suka kama gabansu.
Gwamnan ya kai ziyara makarantar ranar Litinin da misalin karfe 6:45 na safe kamar yanda kafar Pointblacknews.com ya ruwaito.
Kafar tace wani jami’in tsaro ya bayyana mata cewa, gwamnan ya zargi wasu jami’an tsaro da yin sakaci har aka sace daliban su 25.
Kafar tace Gwamnan yace da jami’an tsaron da aka tura makarantar suka je sai suka buge da daukar hotuna da ‘yan mata daliban makarantar.
Wani malami da ya tsira daga harin ya bayyanawa kafar PointBlacknews.com cewa, abin mamaki ne ace duk da gargadin DSS kuma an kai jami’an tsaro gurin amma harin ya faru.
Ya bayyana cewa, jami’an tsaron sun rika koyar dasu dabarun kariyar kai amma sai suka tafi, bayan tafiyarsu, Mintuna 30 sai aka kai harin.