
Sabon Shugaban jam’iyyar PDP, Tanimu Turaki ya roki shugaban kasar Amurka, Donald Trump da ya gaggauta kawo sauki Najeriya dan ya ceci kasar.
Ya bayyana hakane bayan samun shiga cikin hedikwatar jam’iyyar PDP bayan da jami’an tsaro suka hanashi shiga da farko.
Tanimu Turaki yace Trump ya zo ya ceci Dimokradiyyar Najeriya daga hannun wadanda ke son lalatata.
Yace Ba Mhuzghunawa Kiristoci kadai ake yi a Najeriya ba hadda ma wulakanta Dimokradiyya.
Saidai fadar shugaban kasa ta bakin me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya bayyana cewa wadannan kalaman na Tanimu Turaki cin amanar kasa ne kuma ba za’a manta dasu ba.