Friday, December 5
Shadow

An gano cewa, Wasu Inyamurai ne masu son kafa kasarsu suka kai Rahoton cewa ana Mhuzghunawa Kiristoci a Najeriya zuwa kasar Amurka

Rahotanni sun bayyana cewa, wasu Inyamurai ne karkashin wata Kungiya ta son kafa kasar Biafra suka kai kara kasar Amurka cewa ana yiwa Kiristoci Khisan Kyiyashi a Najeriya.

Rahoton yace kungiyar me suna the United States of Biafra da sauran wasu kungiyoyin dake karkashinta sun mika wannan korafi ne ga Hukumar FARA ta kasar Amurka.

Sannan Sanatan kasar Amurka, Ted Cruz ya taimaka musu wajan yayata wannan magana inda yace babu inda akewa Kiristoci Khisan kyiyashi kamar a Najeriya.

Lamarin dai ya watsu sosai musamman a kafafen sada zumunta.

Saidai Tuni Gwamnati ta musanta wannan rade-radin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ana ta sukar Malam Aminu Ibrahim Daurawa ciki hadda 'yan Izala saboda amsar da ya baiwa wata mata data tambayeshi halascin Shugabancin mata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *