
Wani dan kudu kuma Kirista me suna Oyemyke ya bayyana cewa, shi bai yadda ace musulmai ne suka kai Harin cocin jihar Kwara ba.
Harin cocin jihar Kwara wanda ya faru a Bidiyo kai tsaye, ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta inda akaita Allah wadai dashi.
Saidai Oyemyke yace ba musulmai bane, yace yayi hulda da musulmai da yawa yasa ba zasu rika aikata irin wannan abu ba.
Yace ‘yan siyasa ne kawai ke aikata wadannan abubuwan dan cimma burinsu.