
Bidiyon wasu ‘yan mata a cikin motocin Alfarma, Sojoji da yawa na musu rakiya hadda jirgin sama ya dauki hankula sosai.
Da yawa sun bayyana cewa, wannan abu ya nuna shuwagabannin Najeriya kansu da iyalansu kadai suka dau dasu basu damu da tsaron Talakawa ba.
Rahotanni daban-daban wadanda basu tabbata ba na cewa ‘ya’yan karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ne.
‘Yan matan dai sun rika Fariya suna nuna irin rayuwar kece raini da suke ciki.