Friday, December 5
Shadow

Duk Wanda yayi farin ciki da zuwan Amurka Najeriya, ya kafurta>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Babbab malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa, duk wanda yayi Murna da zuwan Amurka Najeriya ya kafurta.

Ya bayyana hakane a wajan wa’azinsa da yake yi a masallacin Sultan Bello ranar Juma’a.

Malam yace ko zuwan Amurkar da tace zata zo ta ceci Kiristoci ba abinda zai kawota kenan ba, suna neman inda zasu saci man fetur ne.

Malam ya kara da cewa, niyyar Kisa kawai ta isa ta kai mutum zuwa wuta.

Malam yace akwai hadisi dake cewa, a karshen Duniya, za’a rika kashe mutum wanda yayi kisan bai san dalili ba hakanan wanda aka kashe shima bai san dalilin ba.

Karanta Wannan  Kalli Hotunan Tauraruwar fina-finan Hausa Mufeeda sun jawo cece-kuce sosai wani yace "Dan Allah a rika rufe Rufaida"

Malam yace kuma Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)yace da wanda yayi kisan da wanda aka kashe duka ‘yan wuta ne.

Malam yace hadda wanda yake son a rika yin kisan, misali masu son a shiga daji a kashe kowa saboda ‘yan ta’addane, malam yace duk wuta zasu.

Malam yace wanda zai tsira shine me son a yi Sulhu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *