
Tauraron kwallon Kafa, Cristiano Ronaldo ya dauki hankula saboda kwallon da ya ci ta hanyar tasshi sama ya daka alkafura.
Ronaldo ya saba cin irin wannan kwallon amma abinda ya dauki hankulan mutane shine a yanzu yayi hakanne a yayin da yake da shekaru 40 wanda ba kowane dan kwallo ne ke iya yon hakan ba.
Da yawan masoyansa sun ta yaba masa akan wannan namijin kokari.