
A makon da ya gabata ne Najeriya ta yi fama da hare-hare mafi muni kan makarantu cikin ƙanƙanin lokaci.
A ranar litinin ƴan bindiga sun far wa makarantar kwana ta ƴan mata da ke garin Maga a jihar Kebbi, tare da sace ɗalibai 25.
Kwanaki ƙalilan bayan nan, a ranar juma’a, wasu ƴan bindiga a kan babura suka shiga makarantar kwana da St Mary da ke garin Papiri a karamar hukumar Agwara da ke jihar Neja, suka sace ɗalibai da malamai da ake hasashen sun kai 300.
Ƴan ƙasar na ci gaba da bayyana fushin su kan yadda ake ci gaba da samun ƙaruwar hare hare a makarantu da sace ƙananan yara.
Sai dai har yanzu gwamnatin ƙasar na nanata cewa ta na ɗaukar matakan dawo da waɗanda aka sace, amma har yanzu ba ta kai ga nasara ba, sai dai akwai waɗanda rahotanni suka bayyana cewa sun tsere.
Wannan ne ya sa jihohin da lamarin ya faru, da ma wasu jihohin da ke makwaftaka da su ko kuma waɗanda ke fama da matsalar tsaro suka fara ɗaukar matakin ‘kariya’ ta hanyar rufe makarantun jihohin, musamman makarantun kwana.
Ga jerin jihohi 8 da suka rufe makarantu a yankin Arewa:
Jihar Kebbi
Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da rufe duka makarantun jihar na gwamnati da masu zaman kansu.
Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da Kwamishinan ilimi mai zurfi jihar, Alhaji Issa Abubakar-Tunga, da takwararsa ta ilimi a matakin farko, Dokta Halima Bande suka fitar, sun ce matakin ya kunshi makarantun sakandire da na gaba da sakandire da ke faɗin jihar.
Sanarwar ta ce matakin ya zama wajibi sakamakon samun matsalar hare-hare cikin wasu sassan jihar a baya-bayan nan.
Matakin ya shafi duka manyan makarantun jihar, in ban da kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma da ke binrin Kebbi, babban birnin jihar, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.
Jihar Katsina
Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe duka makarantun sakandiren faɗin jihar saboda dalilai na tsaro da satar ɗalibai a wasu jihohi.
Kwamishinan ilimi na jihar Hon. Yusuf Sulaiman Jibiya ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ta ɗauki matakin ne saboda abubuwan da ke faruwa a maƙwabtan jihohi na satar satar ɗalibai.
Ya ƙara da cewa rufe makarantun na wucin gadi ne, bayan komai ya daidaita za su umarci ɗaliban su koma makarantun domin rubuta jarrabawar ƙarshen zango, wadda ita ce dama yanzu ta rage.
Jihar Yobe
Gwamnatin jihar Yobe ya bayar da umarnin rufe duka makarantun sakandiren kwana da ke faɗin jihar saboda barazanar tsaro.
Cikin wata sanarwa da babban darakta yaɗa labaran gwamnan jihar, Mamman Mohammed ya fitar ya ce gwamnatin ta ɗauki matakin ne domin kare ɗaliban da ke makarantun kwana.
Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bayan taron ƙoli na tsaron jihar da Gwamnan Mai Mala Buni ya jagoranta, domin nazarin tsaron makarantu a wasu sassan ƙasar.
Jihar kwara:
Gwamnatin jihar Kwara ta bayar da umurnin rufe dukkanin makarantun da ke wasu ƙasanan hukumomi huɗu da ke jihar.
Ƙungiyar malamai ta ƙasa NUT, reshen jihar ta Kwara ce ta sanar da matakin saboda ƙaruwar matsalar tsaro a wasu yankunan.
Shugaban hukumar Yusuf Agboola, ya ce za a rufa makarantu a ƙananan hukumomin Isin da Irepodun da Ifelodun da kuma Ekiti.
Jihar Naija
Gwamnatin jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya ta sanar da rufe duka makarantun da ke faɗin jihar sakamakon sace wasu ɗaliban makarantar St. Mary mai zaman kanta a garin Papiri na karamar hukumar Agwara.
Gwamnan jihar Umaru Bago ne ya sanar da haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar.
Umaru Bago ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da ceto ɗaliban tare da maido su cikin kwanciyar hankali.
jihar Taraba
Gwamnatin jihar Taraba ta bai wa dukkanin makarantun gwamnati da masu zaman kansu na kwana umurnin su koma na tsarin jeka ka dawo.
A cikin sanarwar da gwamnatin ta fitar a shafinta na X, ta ce matakin ya biyo wani nazari da ta yi kan tsaro wanda ya duba lamurran da suka faru a baya bayan nan a jihohin Kebbi da Neja.
Ta ce rahoton nazarin ya nuna ɗaliban makarantun kwana a matsayin waɗanda suka fi zama cikin barazana.
Jihar Bauchi:
Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da rufe dukkanin makarantun firamare da sakandire da manyan makarantu na gwamnati da masu zaman kansu.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce ta ɗauki matakin ne bayan yin shawarwari mai zurfi sakamakon matsalolin tsaron da ke shafar ɗalibai da malamai da makarantu.
Jihar Filato.
Ma’aikatar ilimi ta jihar Filato ta bayar da umarnin rufe duka makarantun jihar na furamare da sakandire sakamakon ƙaruwar matsalar satar ɗalibai a ƙasar.
Hukumar Ilimi a matakin farko ta jihar, PSUBEB ta bayyana ɗaukar matakin a matsayin matakin kariya ga ɗaliban jihar.
Ma’aikatar ilimin jihar ta ce matakin na wucin-gadi ne kuma ya zama dole, la’akari da halin da ake ciki.