
Wannan matar wadda mijinta Soja ne ta koka da cewa Wai Brigadier general ne ya rasa rayuwarsa a irin wannan hanyar amma shiru kake ji.
Tace lokacin shna yara idan kurtu ya rasa rayuwarsa ta irin wannan hanyar ba karamin tashin hankali ake shiga ba, za’a rikita gari ne kowa sai ya shaida.
Tace amma abin takaici ji kake shiru an kashe me mukamin Brigadier General.
Ta yi kira ga shugaba Tinubu ya dauki mataki kan lamarin.