Friday, December 5
Shadow

Fàrgàbàr tsàrò ta faru a makarantar Government Girls College, Maiduguri

Rahotanni daga makarantar Government Girls College, Maiduguri dake jihar Borno sun bayyana cewa, An samu fargabar tsaro a tsakanin daliban makarantar.

Rahotanni sun ce lamarin ya farune da daren ranar Litinin inda Daliban suka suka fita da gudu suna cewa sun ga wasu sun shiga makarantar.

Saidai Hukumomin makarantar sun bayyana cewa jita-jita ce kawai ta faru sun yi bincike babu wata fargabar tsaro a makarantar.

Hakanan hukumar ‘yansanda ta jihar ma ta tabbatar da cewa babu wata matsalar tsaro da ta faru a makarantar.

Hakan na zuwane a yayin da ake fama da satar dalibai a makarantu daban-daban na Arewa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: An yaye jami'an tsaro na musamman guda 380 da za su yi yaki da masu kwacen waya a Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *