
Dan gidan tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai watau Ibrahim El-Rufai ya bayyana cewa tun yana dan shekaru 8 ya bar addinin Musulunci ya koma irin wadanda basu yadda da Allah ba wanda a turance ake kira da Atheist.
Ibrahim ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya saki a shafinsa na sada zumunta wanda tuni Bidiyon ya karade kafafen sada zumunta ake ta Muhawara akai.
Ya kara da cewa ya dauki wannan mataki ne bayan da Allah ya dorawa ‘yar uwarsa cutar kwakwalwa wadda ta yi sanadin mutuwarta sannan ya dauki rayuwar dan uwansa a hadarin mota.
A jiya dai, Hutudole ya kawo muku inda dan gidan El-Rufai din ke cewa Hausawa su daina Bibiyarsa shafinsa na sada zumunta inda yace bashi da wata alaka dasu.
Sannan yace yana saka sarqa, yana kitso, yana kuma saka barimar hanci.