
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, Hukumar ‘yansandan birnin ta baiwa jami’an ta dake baiwa manyan mutane kariya da su janye su je ofis ana nemansu.
Hakan na zuwane bayan da gwamnati ta sanar da shirin janye jami’an ‘yansanda daga baiwa manyan mutane a Najeriya tsaro dan a mayar dasu aikin da ya kamata su yi na bayar da tsaro.
Daga cikin manyan mutanen da aka janyewa jami’an tsaron akwai su tsaffin mataimakan shugaban kasa, Atiku Abubakar da Namadi Sambo, da Matar tsohon shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari, da Ministan Abuja, Nyesom Wike da sauransu.