
Shugaban ‘yansandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya bayyana cewa maganar janye ‘yansanda daga baiwa manyan mutane tsaro abune wanda ba gudu ba ja da baya.
Ya bayyana hakane a wata ganawa da manema labarai da yayi.
Yace dama can suna haka amma tunda yanzu Umarni ya zo daga wajan shugaban kasa, babu wani Minista ko Gwamna da zai kirashi da sunan neman Alfarma.
Yace ya ga ana ta yada wani labari wai akwai ‘yansanda 130,000 dake baiwa manyan mutane tsaro a fadin Najeriya, yace ba gaskiya bane hakan.