
Wasu ‘yan Bindiga 3 sun yiwa karamar yarinya me shekaru 13 fyàdè a kauyen Kudodo dake yankin Galko na karamar hukumar Shiroro jihat Naija.
Wani dan jam’iyyar APC a jihar Naija, Babangida Wassa Kudodo ne ya bayyana hakan.
Yace lamarin ya nuna irin yanda rashin tsaro ke kara munana a jihar.
Tuni aka kai yarinyar Asibiti dan kula da lafiyarta.
Jihar Naija na daga cikin jihohin Arewa masu fama da matsananciyar matsalar tsaro.